Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|


IDRIS AL’HUSAINI
(Maroko – Bamalike)An haife shi a garin “Maulaya Idris” a shekarar 1967, ya rayu a garuruwan Maroko, a kasrul kabir, da maknas, da ribad, saboda tiransifa ta ayyukan babansa na ma’aikatar noma da yake yi.
Ya rayu a cikin iyali da yanayi na jama’ai wayayyiya da son ‘yanci da tunani da hankali.
Yana cewa: Na rayu a cikin gidan dab a a dukan yaran gida sam, domin mu ‘yan maroko ba mu san yadda zamu doki yaranmu ba, mun kasance da ‘yancin duk wani tunani gaba daya, wannan ‘yancin ya taimaka mini shiga cikin duk wata gwagwarmayar tunani ba tare da wani tajriba da ta gabata ba.
Kamar yadda akwai ‘yancin tunani a Maroko ta yadda kowa yana iya daukar tunanin da yake so ba tare da tsangwama ba matukar bai kawo rudu da yamutsi a cikin al’umma da tsaronta ba.
A wannan yanayi ne Sayyid Idris ya rayu yana mai siffantuwa da hankali, kuma duk abin da yake tare da shi na tunani ya fadada.

Farkon bahasi

Da farko ya fara gane cewa babu wani abu da ya shafi addini sai yana da alaka da tarihi, kuma dukkan abin da musulmi suke da shi na akida, da hukuncin shari'a, da wayewa duk ya zo ne ta hanyar ruwaya, don yana ita kuwa ruwaya ta dogara da tarihi ne, don haka sai ya ga bari ya karanta tarihin al'umma wanda yake mafi muhimmancin madogara, kuma ba tare da wani bangaranci ba.

Fuskantar Wahalahu

Farkon wahalar da Sayyid Idris ya fuskanta ita ce ta gargadin malamai a kan ya daina binciken al'amuaran tarihi da suka jima a kwance, suna cewa wannan babu wani abu da zai haifar sai fitina da raunana akida. Sai dai nan da nan sai ya keta wadannan shingen da aka gindaya ya kutsa cikin tunani da binciken tarihi ba karbi wancan tunanin ba. Yana cewa: Binciken gaskiya ya zama fitina a wurin mutanen, kuma suna ganin ya fi kyau a zauna a cikin rudu da boye gaskiya da a yi binciken hakikanin abin da wahayi ya zo da shi, kai ka ce addini yana son zuwa da boye gaskiya da rudu ne.
Yana cewa; matsala ta biyu da ta sha gabansa ita ce ta tsarkake wasu mutane da ba su kima, sai dai daga baya ya gane cewa gaskiya ta fi mutane daraja da kima kuma dole ne ya kutsawa neman wannan gaskiya, don haka bai ba wa tsarkake wasu mutane damar sandarar da tunaninsa ba har ya hana shi binciken gaskiya. Ya kutsawa bincike yana mai cewa: Na yi duk abin da zan iya na neman gaskiya kuma na dagae akan hakan duk da wahala da tsanani.

Sanin Shi'a'nci

Yana cewa: Na samu wasu littattafai guda biyu game da al'amarin Karbala da kuma tarihin Imam Ali (a.s), kuma shi ne karo na farko da na samu irin wadannan littafai, sai dai na dage a kan karanta su, kuma ban yi tsammanin cewa marubutan wadannan littattafai Shi'a ba ne , domin ban taba zaton cewa Shi'a musulmi ba ne. sai ya kasance ba na iya bambance mas'alar Shi'a da Budawa da Shaikhiyya.
Daga nan ne sai tunanin na ya bude na gane wasu ra'ayoyi na Shi'a'naci, sai na fara tambayar to don me su wadannan suke Shi'a mu kuma Sunna, daga nan ne fa sai na fara samun wani tunani yana zo min ina kaikawo a cikin tunanina koda yaushe, sai na neman mantar da lamarin domin in samu saukin bincike, sai da wannan kokwanto da tunani mai karfi da yake bijiro mini ya hana ni kawar da mas'alar daga tunanina.
Ya ce: Amma sai na kanne na ci gaba da binciken domin in samu amsar wadannan tambayoyi da suke cikin kwakwalwata. Ya ce: Ba a dade ba sai na gano wani sirri na kage da 'yan Sunna suke yi wa duk wani wanda ba a kan tafarkin su yake ba kamar dai kage da suka yi a kan Shi'a yana da matukar muni da yawa, ga kokarin toshe gaskiya da boye ta domin kada na baya su gano abubuwan da suka faru a tarihi, ya ce: mafi girman mas'alar da ta sha boyu a tarihi ita ce ta waki'ar Karbala, da gane wannan lamari ne ya gano cewa; lallai dole ne al'ummar musulmi ta samu kanta a cikin wannan bala'in da take cikinsa a yau a hannun azzaluman mutane, kuma ya gano cewa wannan zaluncin da yake faruwa yana da asasi tun farkon faruwar wannan al'umma.

Bala'in Mafi Yawa

Duk sa'adda na kawo wata tambaya sai wani shedan ya ce da ni ka bar wannan mas'alar kada ka bincika ta, ko ka fi sauran miliyoyin musulmi ne da suka ki bincikawa, ko kuma ka fi su sani ne da zaka yi karambanin kutsa wa wannan lamarin. Ya ce: Sai dai ni na san wadannan miliyoyin ba su tambayi kansu irin tambayar da na yi wa kaina ba, haka nan dai wadannan tunaninnika suka so in bar wannan mas'ala amma dai haka na ci gaba da bincike domin in samu amsar abin da yake damu na.
Haka nan na kawar da tunanin mafi yawa da kawar da girman yawa a tunanina na shiga binciken gaskiya kuma na ga cewa lallai ba yadda za a yi mafi yawa ya kasnace ma'aunin gaskiya a gaban wadannan tunani da ra'ayoyi masu rikitarwa.
Ya ce: sau da yawa nakan kawo wa abokaina mas'alar Imam Husain (a.s) da alayen Annabi (s.a.w) da kuma nuni da abin da na gani a kan cewa yaya nagarin farko zasu kashe alayen Annabi (s.a.w) kisan gilla na kare dangi, yaya sahabbai zasu kuntata wa alayen Annabi haka, yaya babu wani wanda ya yi burin shiga wannan jirgin na tsira na Ahlul Baiti (a.s) har aka fifita jiragen wasu a kan nasu?!.
A nan ne na fara samun kaina ina fizguwa zuwa ga wannan mazhabin na Ahlul Baiti (a.s) ina mai karkata zuwa ga fahimta da dukkan dagewa da dakewa, na samu kaina cewa ba na son in kasance cikin wadannan da suke son yin bacci ko narkewa, kuam matukar ban samu amsa ta ba to ba ni da wani hutu a kan hakan. Sai na fahimci kimar kokari da bayar da himma da kuma matukar bukatar fita daga gado domin fahimtar gaskiya, da kimar cire rigar al'ada da gado. Sai na yi kyakkyawan shiri da tanadi domin fara tafiya zuwa ga tafarkin gaskiya, na samu yayewar kwantsa daga idanuwana, har ta bayyana gareni cewa Shi'a'nci shi ne addinin da ya zo daga Allah madaukaki tun farkon musulunci, sauran mazhabobi su ne rarraba da ta zo daga baya suka bi wadanda ba su ne Allah ya ce a bi ba.

Matakin Karshe

Sayyid Idris ya ce: Daga karshe bayan gaskiya ta bayyana gareni sai kuma na fada cikin fada tsakanin raina da hankalina, raina tana ganin wahalar cizge hakurin al'adu mai wuyar fita, yayin da hankali yake ganin gaskiya ta fi cancanta da biyayya, wannan shi ne mafi wahalar lamarin da na zartar a rayuwata domin in canja tunani da ra'ayi da akida da mazhaba.
Daga karshe dai sai na zabi shiriyar ma'abota tsarki alayen gidan Annabi (s.a.w), kuma na shelanta mazhabata sabuwar fahimta a Maroko, sannan sai na tafi Damaskus kasar Siriya domin ci gaba da karatuna a can, na samu ilimi a hannun malamai masu dama, kuma har yanzu ina bin karatuna na Hauza domin koyon ilimi hada da ayyukan da nake yi na jarida da rubutu.
Sayyid idrisa ya himmantau da abubuwa biyu; da suka hada da binciken ilimi da sababbin maudu'ai da ake tattaunawa, da kuma binciken mazhabobi da addini, kuma zuwa yanzu ya rubuta littattafai masu yawa kamar "Lakad Shayya'anil Husain" wato Husain ne ya shi'antar da ni, da sauran littattafai kamar "alkhilafatul Mugtasaba" da sauran littattafai.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
9+4 =