Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|


AA’AD WAHID AL’QASIM
(Bapalasxine - Bahanife)An haife shi a palasxin shekara ta 1965 daga gidan da suke riqo da mazhabar hanafiyya, kuma ya samu shedar digiri a ilimin fasahar qere-qere da digiri na biyu a kan tafiyar da al’amuran qirqire-qirqire, da kuma digiri na uku a kan tafiyar da al’amura al’umma.
Wasu littattafai da suke sukan mazhabin ahlul bait (A.S) su ne suka sanya shi binciken littattafan Shi'a sannan sai ya duba abin da ya zo a cikin sihahus sitta, kuma wannan lamarin ne ya kai ga shiga shianci bayan bincike da ya kai shi shekaru biyu.

Na farko game da saninsa da shi’anci

Daktra sa’ad yana cewa: na fara karanta savanin mazhabobi a shekara ta 1978 lokacin ina karatu a jami’ar Pilipin, bayan na ga irin yadda wasu suke kafiratawa ga Shi'a da shianci.

A wannan lokacin sai ya kasnce ba ni da wata manufa sai neman karanta irin waxannan mas’alolin na savani saboda ba na jin akwai wata buqatar saninsu, kuma dukkan abin da na sani game da Shi'a shi ne su musulmi ne da suke da savani da ahlussunna a wasu mas’alolin da bai kai ga kafirta su ba, kamar fifitawar da suke wa Ali (A.S) kan sauran sahabbai, da himmantuwarsu da ziyarar kaburburar imamai (A.S), don haka sai na kasance bana ganin akwai wata buqatuwa sanin bincike tsakanin Shi'a da Sunna, domin ban san cewa akwai wata natija da za a samu ba sakamakon irin wannan binciken.

Dakta as’ad ya kasance yana da wani ra’ayi na ganin cewa dole ne a samu warware matsalar da take tsakanin musulmi ta hanyar binciken gaskiya ba tare da an tayar da jijiyar wuya ba sannan sai mu yi aiki tare da abin da ya haxa mu, kuma mu nisanci abin da ya rarraba mu, kumma wannan yana iya samuwa ne kawai ta hanyar bincike ba tare da fusata ba ko zafafawa kuma kowa ya girmama xayansa domin ya kasance an samu bincike ba tare da faxawa cikin vangaranci ba da son rai, don a samu yanayin da zai sanya mu ganin gaskiya a fili, kuma a samu haxuwa tsakanin ma’abota mazhabobi daban-daban sai kowa ya bijiro da abin da yake gunsa, kuma wannan ra’ayin ya sanya qyamatar sa daga wurin wahabiyawan da suke raba littattafai kullum kan kafirta Shi'a da nuna wajabcin nisantarsu, kuma suka matsa masa kan cewa dole ya bar irin wannan tunanin.

Yana cewa; wannan al’amarin ya sanya neman tilasta shi imma dai shi ma ya xauki matsayin kafirta Shi'a ba tare wani dalili da yake da shi ba kuma ya rufe idanuwansa ya makance , imma kuma ya kasance Shi'a kawai domin babu wani mataki da yake tsaka-tsaki. Wahabiyawan sun kasance suna takura shi a kan hakan kuma kodayaushe suna raba littattafan da suke kafita Shi'a ga xalibai da suke nuna cewa haxarinsu ya fi na yahudawa.

Ya ce; wannan lamarin sai ya sanya ni binciken abin da yake wakana domin in samu amsar mas’aloli masu yawa da suke cikin qwaqwalwata, musamman abin da ya shafi halifanci bayan Annabi (S.A.W).

Samun amsar bincike game da shianci

Bayan Dakta as’ad ya karanta littattafai masu yawa sai kuma ya fara karanta littattafan Shi'a domin ya ga amsar da suke bayarwa kan waxannan mas’alolin musamman littafin muraji’at wanda yake qunshe da muhawara tsakanin malamin Sunna na azhar da malamin Shi'a.
Ya ce: sai na samu cewa Shi'a suna kafa hujja ne ma da ayoyin kur’ani da hadisai da suke cikin ingantattun littattafan Sunna kansu kamar su sahihul buhari da sahih muslim.

Saboda qarfin hujjar da suke kawowa daga waxannan littattafai har sai da na samu wasu daga masu da’awar wahabiyanci da suka yi mini alqawarin idan da gasket akwai waxannan al’amuran a cikin buhari to lallai a shirye suke suk kafirce da littafin savanin yadda malaman Sunna suke ganinsa.
Kuma tun da babu wanda yake da kwafi na buhari sai na yi qoqari na samu guda xaya daga ma’ahad dirasatul islamiyya a xayan jami’o’in Pilipin, sannan sai na koma na duba waxannan ruwayoyi don in tabbatar sai na same su kamar yadda aka yi nuni da su, sai na samu yaqini da ingancin da’awar Shi'a na cewa halifofi bayan Annabi (S.A.W) su ne imamai goma sha biyu ne da suka fara tun daga Ali (A.S) har zuwa kan Imam mahadi (A.S).

Wuce marhalar canjin mazhaba

Don haka ne sai ya canja mazhaba ya bar ta ‘yan ahlussunna, ya ce da farko ban gane cewa dole ne in bar mazhabar sunnanci ba kuma ba na tunanin na bar shi, kuma ban xauka yarda da wannan tunani na halifancin Imam Ali (A.S) yana nufin na bar mazhabata ba, sai dai kawai ina ganinsa a matsayin wani lamari ne na tarihi mai muni matuqa.

Idan mazhaba tana nufin riqo da sunnar Annabi (S.A.W) to sanina da ahlul bait (A.S) ya qara mini riqo da sunnar Annabi (S.A.W) domin su ne mafi kusancin mutane zuwa gareshi. Amma duk da haka sai suka riqa kira na da cewa; ni Shi'a ne kuma ni ban damu da hakan ba domin ban da wani mummunan ra’ayi tun farko game da hakan. Musamman da yake ba na ganin musulmi bisa asasin mazhaba, sai dai asasin aiki nagari da ikhlasi.

Abin da ya biyo baya

Yana faxa game da abin da ya gamu da shi na tsanani daga danginsa cewa; ban tava tunanin cewa zan samu matsala da dangi ba domin ina ganin al’amari ne na kaina kawai da Allah maxaukaki zai yi mini hisabi a kai idan mai kyau ne ko mummuna, kuma sai na samu da godiyar Allah cewa; dangina suna da fahimta mai kyau kan hakan kuma ina da alaqar so tsakanina da su.

Amma game da al’umma ba mu gushe ba har yanzu suna da ta’assubanci da vangarancin mazhaba da addini kuma wannan wani abin qi ne da qyama a wurinsu, a cikin al’ummarmu har yanzu addini wani abu ne da ake gadonsa, wannan lamarin ne ya sanya ni rasa wasu abokai, sai dai kuma na samu wasu, kuma dayawansu masu neman sani ne kuma wannan ne ma ya sanya ni jituwa da su, sai dai wayewa da sauyi wani abu ne wanda yake buqatar lokuta.
Ya wallafa littattafai masu yawa har zuwa yau da an buga wasu daga cikinsu.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
3+8 =