Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|


DR. TAJUDDIN AL\'JA\'UNI
(Jodan – Sunna)An haife shi a mamallakar sarautar Jodar Alhashimiyya a babban birnin kasar Amman, ya yi karatu har ya kai ga shedar Babban Digiri na uku a likitancin mata, kuma duk da haka yana son karatun addini, don haka ya bayar da lokacinsa mai yawa domin karatun addini, don haka ne ya gama makarantar likitanci tare da kyawawan halaye da kuma ilmi da imani da ladabi, kuma a samkamakon haka sai ya wallafa littafai mai juzu'I hudu wanda yake da taken "mutum wannan halitta mai ban mamaki" ta yadda ya fitar da hikimomin likitanci da suke kunshe cikin Kur'ani mai daraja.
A nan ne ya hada ayoyi da ilimi ya samara da wani tunani mai fadi game da tunanin addini na zamani, ta yadda mai karatu zai ga yana rayuwa a cikin abubuwan biyu; wato addini da kuma ilimin zamani, hada da abubuwa masu yawa da suka hikimomi da mu'ujizozin kuran'an madaukaki domin kalubalantar wariyar da aka yi wa ilimi da addini kamar yadda tunanin ya shigo daga masu neman dulmuyar da ita domin jama'a mai zuwa ta taso tan mai masaniya da dukkan sirrin ilimin addininta.
Dr Tajuddin bai taba bayar da dama ga karatun likitanci ya hana shi sanin ilimin addini ba, kamar yadda yake cewa: Na kwadaitu matuka wajen sanin koyarwar musulunci da Kur'ani da hadisi domin sanin ilimi domin in sanya shiriyar ilimin addini ta kasance ma'aunin da zan dogara da shi wurin fassara komai. Ina mai riko da fadin Allah (s.w.t) cewa duk wadanda suka yi kokari a cikin lamarinmu to zamu shiryar da su tafarkinmu, da fadinsa cewa: Shin wadanda suka sani zasu yi daidai da wadanda ba su sani ba.
Ta hanyar sanin kansa da addininsa da ubangijinsa da ilimomi ne ya ga bari ya fita daga gado a cikin tunani, kuma da sannu sai ga shi yana kokarin gano hakikanin gaskiyar musulunci ba tare da la'akari da mazhabar da ya gada wurin iyaye ko al'ummar da yake rayuwa cikinta ba

Canja Mazhaba

A cikin bincikensa na ilimi da yake neman gaskiya sai ya yi kokarin ganin fita daga dukkan dogaro da tunanin da ya gada domin samun hakikanin gaskiyar musulunci, bayan bincike mai yawa da zurfi sai ya hango gaskiyar lamari tana bayyana sai ya samu shiryuwa zuwa ga hasken Ahlul Baiti (a.s) wadanda suke su ne zababbun Allah madaukaki.
Sai ya zabi shiriyar jirgin tsira da amincin al'umma kuma hanyar shiriyarta wato alayen Muhammad (s.a.w), wadanda suke su ne dayan alkawura biyu masu girma da nauyi a kan al'umma. Kuma bayan fahimtar wannan ne ya sanya shi kama hanyar ganin ya isar da sakon nan mai girma zuwa ga sauran al'umma, don haka sai ya shiga rubuta makaloli ana buga su a cikin jaridu da suke na kasa domin sanar da mutane tafarkin Ahlul Baiti (a.s).

Daga cikin talifofinsa akwai

"Al'insan hazel ka'inul ajib" wanda aka buga shi a 1993, miladiyya, a Daru Ammar, Jodar, bolum hudu ne. Da littafin nan mai suna "Alma'ud dafik". Wanda yake bayani game da samuwar mutum kamar yadda mafi yawan masu bayanin ilimi suka yi game da kwan namiji da na mace, da bayanin sirrin Kur'ani kan wannan lamari na ilimi da ya kawo tun zamuna masu yawa da suka gabata. A cikin wannan littafin akwai duk wani bayani na siffofin maniyyin namiji da na mace, da nuni da cewa; duk sa'adda muka ga haihuwar 'ya'ya mata to daga miji ne haka ma 'ya'ya mata duk daga miji ne.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
6+4 =