Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Shin Shahad Ta Uku Ga Imam Ali (a.s) Farilla Ce|?


Mafi karancin karancin abin da zai iya sanya mutum ya kasance musulmi shi ne kalmar shahada wacce take kunshe da imani da Allah da manzonsa. Sai dai mun samu wasu daga jama’;ar musulmi musamman Shi'a suna ambaton kalmalar shahada sannan sai su kara da kalma ta uku mai kunshe da imani da cewa imam Ali (a.s) waliyyin Allah ne.
Sannan abu ne gun dukkan musulmi Shi'a da sunna cewa da kalmar shahada biyu na farko mutum yake zama musulmi, kuma dukkan hukuncin musulmi suna hawa kansa, kuma yana da dukkan hakkokin da musulmi suke da shi. Sai dai amma tambaya a nan ita ce; shin akwai wani dalili a kan wannan shedar ta uku ko kuwa?
Shia suna ganin duk da wilayar imam Ali (a.s), da sauran imaman shiriya da manzon Allah (s.a.w) ya yi wasiyya da su (a.s) tana daga asasin addini, sai dai sun yarda cewa rashin imanin da wilayar imam Ali (a.s) da sauran Ahlul Baiti (a.s) ba ya kore musulunci mutum, sai dai ita wannan wilayar tana daga cikin cikar imani ne.
Don haka ne duk wanda bai yi imani da ita ba, musulmi ne, sai dai ya bar wani rukuni babba na cikar imani ne. Muna iya ganin manzon Allah (s.a.w) ya yi wa musulmin da suka ki bin umarninsa na kawo masa tawwada da takarda da zai yi rubutu hukuncin musulmi duk da kuwa kin umarninsa yana daga cikin kaba’ira sabo mai girma, kuma yana kai mutum ga shiga wuta. Kuma mafi muni shi ne; wannan rashin biyayyar ga manzon rahama (s.a.w) ya kai ga bacewar al’ummarsa daga abin da ya bar ta a kansa na wasiyyarsa da biyayya ga wadanda ya bar wa al’umma. Amma duk da haka sai ya kore su daga gidansa, bai kuma kafirta su ba, ya yi musu hukuncin musulmi ne. Duba Sahihui buhari: 1/37.
Sannan ya gaya wa imam Ali (a.s) cewa; wannan al’ummar tasa zata yaudare shi, ta ki biyayya ga imam Ali (a.s) bayansa, sannan ya umarce shi da ya yi mu’amala da su a matsayin musulmi. Duba; Mustadarak na Hakim; 3/142, da Tarihu Bagdad; 11/216, da Kanzul Ummal; 11/297, 617, da Tarihu Damishk; 42/448.
Don haka ne malaman Shi'a suka tafi a kan cewa; Ba a kafirta wanda ya ki yarda da wilayar imam Ali (a.s) da sauran imamai daga Ahlul Baiti (a.s), sai dai idan ya kasance yana gaba da su ne. Don haka wanda bai karbi wilayarsu ba, kuma baya gaba da su, to musulmi ne, sai dai idan ya kasance yana sanin sakon annabi (s.a.w) sannan ya ki karba, wannan yana iya sanya shi mai raunin imani.
Sannan kasancewar musulmin farko ba su san wannan sakon na kalmar shedawa da jagorancin Ahlul Baiti ba, ba ya cutar da imaninsu, musamman irin wadannan musulmin sun rasu ko sun yi shahada a lokacin da mafi yawancin sakon musulunci bai gama sauka ba, don haka ne kowane musulmi iyakancin abin da ya samu ya yi imani da shi, to da shi ne ake lissafa imaninsa, muhimmin lamari shi ne ya yi imani da abin da manzon Allah (s.a.w) ya zo da shi gaba daya, koda kuwa bai yi zamani da lokacin saukar dukkan sakon ba.
Kamar dai farkon sakon manzon Allah (s.a.w) ne yayin da yake cewa da mutane ku ce: "La'ilaha Illal-Lah zaku rabauta" wannan ba ya nufin daya bangaren na cewa; "Muhammad Manzon Allah ne" (Siratun nabawiyya: 1/462, Ibn Kasir) ba ya cikin kalmar shahada.
Sannan wannan shedar ta wilayar Imam Ali da aka fi sani da sheda ta uku, dukkan malamai ba su bayar da fatawar wajabcin shelanta ta ba, ko cewa; ita wani bangare ne na wajibi a kiran salla, duk da kuwa wata rukuni ce ta cikar imani, don haka ne sai ake kawo shi a kiran salla a matsayin wani bangare da ake son fadarsa duk sa'adda aka ambaci bangarori biyu na farkon kalmar shahada.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
8+7 =