Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Yi mana bayani kan kimar dan Adam a wannan halitta tasa, tsakanin sauran halittu? Kuma yaya dan Adam zai iya fahimtar rayuwarsa?


Gaskiya da Wajibi:
Dukkan wata halitta a wannan duniya tamu, tana da wata siffa ta taimakekeniya da 'yan'uwanta, tana bayarwa da kuma karba daga 'yar'uwan nata. Misali, mutum, dabbobi, tsirrai da dabi'a, duk suna jujjuya amfani tsakaninsu, da suka hada da iskar "odygen" da "carbondiodide", abinci, haske, ruwa....da dai sauransu.
Haka shi ma mutum, yana rayuwa ne cikin iyali da al'ummarsa, yana alaka da sauran mutane kana kuma suna jujjuya amfanoni a tsakaninsu. Don haka yana da hakkoki a kan iyali da kuma al'ummarsa, kamar yadda su ma suke da hakkoki a kansa.... Ko wane mutum yana da hakki, yana kuma da wajiban da suka hau kansa, to amma wannan daidaituwa ta al'ummance da dokoki na al'umma ba za su taba tabbatuwa ba kana kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali ba za su samu ba, har sai an kiyaye wadannan al'amurra....
Hakika duk wanda ya bukaci wani abin da ba hakkinsa ba ne, to ba makawa yana zaluntar sauran mutane ne, don kuwa so yake ya bautar da al'umma. A sabili da haka ne al'umma suke ki da kuma jefar da shi.
Dan'Adam yana da hakkin rayuwa, kamar yadda kuma rayuwar hakkinsa ce, haka nan ma samar masa da abubuwan da rayuwar take bukatuwa da su....sannan kuma yana daga cikin hakkinsa a bude masa hanyoyin ayyuka da kuma 'yancin samun abin hannu da kuma mallaka....kuma hakkinsa ne ya samu nasa rabon na albarkatun kasar da yake raye cikinta....
Muna iya ganin hakkokin dan'Adam a fili cikin fadin Allah Madaukakin Sarki:
"Kuma kasa ya aza ta domin talikai". (Surar Rahman, 55: 10)
Don haka an sanya kasa ne don kowa da kowa ya amfana da ita, kuma ba ya halalta ga wani mutum ya ajiye ta a matsayin kayansa kawai ya hana saura amfanuwa da ita.....
Dan'Adam wani sashi ne na wannan al'umma, yana da hakkin amfanuwa da dukkan abubuwan da suke cikin al'ummarsa....
Hakika kange amfani da alherorin da suke cikin kasa ga wata al'umma ko kuma kungiya da kuma haramta wa wata, zalunci ne da kuma gaba da dokokin rayuwa da kuma ka'idojin adalci.... Alkur'ani mai girma yana tabbatar da wannan ka'ida cikin fadinSa Madaukakin Sarki:
"Lalle Allah Na yin umurni da adalci da kyautatawa....". (Surar Nahl, 16: 90)
Don haka "mutane daidai suke kamar hakwaran matsefin kai", kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fadi.
Lalle babu makawa a duk lokacin da mutane suka yi shiru kan zalunci da kuma babakeren da ake musu, to cutarwar za ta koma ga kowa da kowa ne, daga karshe sai ya zamanto wata kungiya ta azzalumai ta hau kan dukkan al'umma da kuma raunana ta.
Don haka, kamar kowane mutum yake kokari wajen sama wa kansa 'yanci, haka nan ya za ma wajibi a kansa ya yi kokari wajen samar wa sauran mutane ma, kada ya takaita shi ga kansa kawai.
Sannan kuma yana daga cikin hakkin dan'Adam ya rayu cikin tsaro da kwanciyar hankali, shi da dukiyarsa da kuma dukkan abin da ya mallaka, hana shi wannan 'yanci kuwa zalunci da babakere ne wanda mai aikata hakan ya cancanci azaba.
Kana kuma kamar yadda hakan ya zamanto 'yancinsa, haka nan ma ya zamanto 'yancin wasunsa ne....don haka a duk lokacin da ya yi wasa da tsaron lafiyar wasunsa, ko kuma ya aikata wani abin da zai tsoratar da su, ko kuma ya haifar da rashin tabbas da kwanciyar hankali a cikin mutane, to ba
makawa ya zamanto abokin gaban al'umma, kuma hakan ma wasa ne da tsaron kan kansa shi ma.
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tabbatar da ka'idar tsaro da kwanciyar hankalin al'umma cikin fadinsa cewa:
"Musulmi dan'uwan musulmi ne, don haka kada ya cutar da shi, ko ha'intarsa ko ya fadi mummunar magana dangane da shi. Sannan kuma jininsa ba ya halalta a gare shi, haka ma dukiyarsa sai da yardarsa (1) ". [1]
Daraja da daukakar dan'Adam tana ga mutumci da karamarsa ne, don haka shari'ar Musulunci ta haramta giba, bata suna, yada kararraki da zubar da mutumcin mutum ta hanyar magana ko aiki ko kuma ta hanyar bincike da bayyana asirin mutum da dai sauransu.
Wannan doka ta Musulunci tana wajabta wa mutum girmama mutumcin sauran mutane, kan kuma ba ya halalta ya keta hurumin sauran mutane....
Allah Madaukakin Sarki Yana ce wa: "Ya ku wadanda suka yi imani! Kada wadansu mutane su yi izgili game da wadansu mutane, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (masu izgilin), kuma wadansu mata kada su yi izgili game da wadansu mata mai yiwu-wa ne su kasance mafifita daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jefi juna da miyagun sunaye na lakabobi. Tir da suna na fasicci a bayan imani. Kuma wanda bai tuba ba, to, wadannan su
ne azzalumai. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku nisanci abu mai yawa na zato. Lalle sashen zato laifi ne. kuma kada ku yi rahoto, kuma kada sashenku ya yi gibar sashe. Shin dayanku na son ya ci naman dan'uwansa yana matacce? To, kun ki shi (cin naman). Kuma ku bi Allah da takawa.
Lalle Allah Mai karbar tuba ne, Mai jin kai". (Surar Hujurat, 49: 11-12)
Haka nan kuma mutum yana da wasu hakkoki a kan al'umma da kuma kasarsa, wadanda gwam-nati ce take daukan mafiya yawa daga cikinsu; wadannan hakkoki sun hada da bayar da ilimi, tarbiyya, kula da samar da tsaro, kiwon lafiya da dai sauransu....Kamar yadda kuma kasa da al'umma suke da wasu hakkoki a kan mutum, kamar su kiyaye maslahohin al'umma da kuma kare su, bugu da kari kan wajiban da suka hau kansa wadanda doka ta yi bayaninsu, wadanda matukar dai bai kula da kuma kiyaye su ba, to rayuwar al'umma za ta kasance tana fuskantar matsaloli da kuma rugujewa. A irin wannan hali shi ma ba zai tsira daga bala'in da zai fada wa sauran al'umma ba.

Ya Ya Za Mu Fahimci Rayuwa?

Wannan rayuwa da muke cikinta....ya ya za mu iya fahimtarta?....kana kuma ya ya za mu yi mu'amala da ita? Rayuwar dan'Adam ita ce ayyukan jiki, tunani da na ruhi da mutum yake aikatawa tun daga haihuwarsa har zuwa mutuwarsa. Kuma ta hakan ne yake tabbatar da samuwarsa da kuma cika zati, ruhi da kuma yanayinsa....
Yakan cika hakan ne kuwa ta hanyar abubuwan da ya mallaka, na daga rayuwa, hankali, karfin yanayin abubuwan da suke kewaye da shi, jin dadi da kuma ciwo, gano abubuwan halitta da hankalinsa yake yi....da dai sauransu.
Hakika mun kasance muna ci da sha, muna sa tufafi, muna wasa da jin dadin kyawawan abubuwa, muna yin jima'i, muna jin soyayya da kiyayya, farin ciki da bakin ciki, jin dadi da kuma jin zafi, muna dariya da kuka, mukan yanke kauna kan al'amurra da kuma burace-burace....
Sannan kuma mukan yi tunani da kuma kirkiro abubuwa, mukan gano sabbin abubuwa sannan kuma mu sanya wasu, kuma mukan yi bayanin abubuwan da suke damunmu ta hanyar magana, rubutu, wake, farin ciki da kuma bakin ciki.
Kana kuma mukan gano abubuwan da suka fita daga wannan duniya tamu ta hanyar hankali da kuma tunaninmu, muna masu tunanin girmansu da kuma yadda aka samar da su. Kuma mukan gano ka'idojin samuwa da kuma Wanda Ya samar da ita....
Hakika mun kasance muna tunani, muna ji, muna aiki, kuma mukan tsara rayuwarmu da tunani da kuma shu'urinmu, da kuma ayyukan da suke fitowa daga gare mu..... Mu mun kasance jiki, ruhi da kuma hankali ne wadanda aka arzurta mu da su.
Mu muke sana'anta rayuwarmu kamar yadda mai zane yake zana hoto rayuwar kowanne daga cikinmu hotonsa ne na zati, to a cikinmu wane ne yake so hotonsa (zatinsa) ya kasance abin kyama....
Hakika rayuwa ba wai jin dadi da annashuwa ba ce kawai, face dai tana hade da abubuwan bakin ciki da dacin rai kuma. Ita ba wai kawai sakaka take ba.... face dai ita nauyi ce....nauyi ce a gaban Allah Ta'ala, nauyi ce a gaban al'umma da kuma mutanen da muke rayuwa da su. Sannan kuma nauyi ce a gaban dokoki, mutumci da kuma samuwa.
Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "Sa'an nan lalle ne Muna tambayar wadanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Muna tambayar Manzannin".(Surar A'araf,7: 6)
Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:"Dukkanku makiwata ne, kuma dukkanku abin tambaya ne kan abubuwan da aka ba ku kiwonsu".
Hakika Ubangijin halitta Ya yi bayanin dabi'ar rayuwa, kuma Yakan buga misalai wadanda za su kusanto da lamurra zuwa ga hankulanmu....Ya yi bayanin cewa ita (rayuwa) aiki ne na girma, daukaka da kuma kamala, kana kuma daga baya ta zamanto abin jefarwa da kuma karewa. To haka rayuwar ko wane mutum a wannan duniya take....
"Ka buga musu misalin rayuwar duniya, kamar ruwa ne wanda Muka saukar da shi daga sama, sa'an nan tsirin kasa ya garwaya da shi, sa'an nan ya wayi gari dudduga, iska tana shikar sa. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan ikon yi ne a kan dukkan kome". (Surar Kahf, 18: 45)
Don haka rayuwa, duk da irin kawa, kyau, jin dadi da annashuwan da ke cikinta, wata aba ce samammiya kana mai karewa, kamar yadda tsirrai sukan girma su yi fure masu kyau, amma daga baya su yi 'ya'ya kana su bushe iska ta debe su....
A lokacin da wannan marhala ta rayuwar mutum ta kare, sai kuma wata sabuwar marhala ta rayuwar tasa ta kunno kai, ita ce kuwa rayuwar lahira. Wannan kuwa ita ce dawwamammiyar rayuwa....duniyar da babu wani canji ko gushewa a cikinta....duniyar ni'ima, kyau da kuma jin dadi, ko kuma duniyar tabewa da kuma azaba.
Hakika abin da ke tabbatar da makomar mutum a wancan duniyar, shi ne yanayin ayyuka da kuma akidarsa a wannan duniya....kamar yadda kokarin dalibi yake tabbatar da sakamakon jarrabawarsa da kuma ci gaban karatunsa.....
Lalle a wannan rayuwa ce mutum yakan share fagen rayuwarsa ta lahira, kamar yadda duniyar mahaifa take share fagen rayuwa duniya. Alkur'ani mai girma ya yi mana bayanin wannan hakika cikin fadinSa Ta'ala ce wa:
"Wanda ya kafirta, to, kafircinsa na kansa, kuma wanda ya aikata aikin kwarai, to, saboda kansu suke yin shimfida". (Surar Rum, 30: 44)
Don haka ne dokokin Ubangiji suka zo don tsara ayyukan dan'Adam da kuma yanayin rayuwarsa.....
Abu ne mai yiwuwa mutum ya bi sha'awace-sha'awacensa, jin dadi da kuma annashuwa, kokuma ji-ji da kai, jahilci ko kiyayya su sami iko a kansa, ta haka sai rayuwa ta kasance wata hanya ce ta biya sha'awa da jin dadi a gare shi. Ko kuma ta kasance hanya ce ta aikata laifuffuka da yada fasadi a bayan kasa da kuma bauta ga jin dadin duniya saboda son zuciya da kuma ji-ji da kai.
Hakika Mahaliccin rayuwa Ya bai wa mutum ita (rayuwa) ce don ya rayu cikin kwanciyar hankali da jin dadin abubuwan jin dadin cikinta da kuma kawaice-kawaicenta, gwargwadon yadda dokokin kiyaye rayuwa da kuma kyautata dabi'u suka tanadar. Ta yadda zai iya tabbatar da alheri a kansa
da kuma al'umma da yake rayuwa a cikinta....
Babu shakka, a lokacin da mutum ya yi kuskuren fahimtar rayuwa, to lalle zai cuci rayuwarsa da kuma ja-gorantarta zuwa ga halaka, kuma da wuya ya iya gane wannan kuskure na sa sai bayan gushewar lokaci.
Don da yawa daga cikin mutane, sha'awoyi, son zuciyarsu da kuma gururi sun kai su zuwa ga halaka da kuma nadama, hakan kuwa bayan kurewar lokaci..
Rayuwar irin wadannan mutane ta kare a gidajen yari daban-daban, kashe kai, kamuwa da muggan cututtukan jima'i (irinsu ciwon AIDS da dai sauransu), shan muggan kwayoyi, damuwa, tabewa da dai sauransu.
Cibiyoyin kididdiga da bincike irin su asibitoci, cibiyoyin lafiya da kuma na muggan laifuffuka sun tabbatar da adadi mai yawan gaske na faruwar irin wadannan laifuffuka a tsakanin al'umma....
Hakika rayuwarmu kyauta ce ta Ubangiji Mai rahama, don haka dole ne mu yi mu'amala da rayuwarmu daidai da dokokin kiyaye lafiya da kuma rayuwa.
Hakan kuwa su ne dokokin Ubangiji, Wanda Ya haramta mana duk wani abin da zai cutar da mu, sannan kuma ya halalta mana dukkan alherori da jin dadin da suke da amfani a gare mu....
Akwai hanyoyi na fahimtar rayuwa, don haka wajibi ne mu koma gare su da kuma dogaro da su. Wadannan hanyoyi kuwa su ne: Littafin Allah da kuma shiryarwar Annabci; wadannan abubuwa guda biyu suna mana cikkakken bayanin rayuwa da kuma hanyoyi da tafarkin shiriya cikin rayuwarmu. Don haka dole ne mu karanta su tare da tunani da kuma cikakkiyar fahimta, don mu san abin da ke cikinsu na alheri da kuma hikima.
Mabubbuga ta biyu na fahimtar rayuwa shi ne ilimi da bincike-bincikensa. Hakika ilimi ya arzurta mu da masaniya da kuma fahimta, ta yadda ya iya bayyana mana abubuwa masu cutarwa da kuwa masu amfanarwa. Sannan kuma wadannan abubuwa da ilimi ya tabbatar da su sai suka yi dai-dai da abin da Alkur'ani mai girma ya tabbatar na haram da halal....
Hakika ilimi ya gano hadarin da ke tattare da giya, muggan kwayoyi, zinace-zinace, cin kudin ruwa, haka nan kuma ya gano fa'idar tsabta, soyayya, sada zumunci tsakanin 'yan'uwa da kuma tasirin da yake da shi wajen kiyaye zaman lafiyan al'umma, da kuma tasirin imani wajen sa'adar dan'Adam, tabbatuwa cikin dabi'u na kwarai, tsira daga damuwa da kuma muggan laifuffuka.....da dai sauransu.
Kamar yadda ilimi kuma ya ba da gagarumar gudummawa wajen daga martabar fahimtar dan'-Adam ga rayuwa, ci gabantar da hanyoyin kerekere da kuma tsara rayuwar al'umma. Ya taimaka wajen biyan bukatun dan'Adam da kuma samo sabbin hanyoyi magance matsalolin rayuwa.
Babu makawa, kirkiro wutan lantarki, man fetur, radiyo da talabijin, hanyoyi rubutu da buge-buge da kuma na safara da dai sauransu, sun bude wa dan'-Adam sabuwar fahimta ta rayuwa. Kuma sanannen abu ne cewa a duk lokacin da fahimta da masani-yarmu da rayuwa ta karu, fahimtarmu ga
addini da ma'anar imani ma za ta karu. Don haka ilimi abu ne da yake kira zuwa ga imani kana kuma abokin zaman rayuwa.
Hankali da kwarewa: Hankali shi ne fitilar dan'Adam a rayuwarsa, don haka a duk lokacin da mutum ya yi amfani da hankali kamar yadda ya dace, to ba makawa zai kai shi ga alheri da kuma tsamar da shi daga halaka, bata da kuma nadama.
Dan'Adam ya kasance mai aikata abubuwa da daman gaske a rayuwarsa, don haka ya mallaki kwarewa daban-daban a rayuwartasa. A saboda haka, ya za ma dole ya yi amfani da wannan kwarewa da ya samu wajen kyautata rayuwarsa, kamar yadda kuma yake wajibi ya yi amfani da kwarewar sauran mutane a dukkan bangarori na rayuwarsa shi kadai, da na aure, tattalin arziki, siyasa, wayewa da dai sauransu.
A saboda haka ne ma, Alkur'ani mai girma ya yi mana umurni da amfani da hankali da kuma kwarewar al'umman da suka wuce. Don kuwa kwarewar mutane da kuma abubuwan da suka faru a baya na tarihi, bugu da kari kan abubuwan da hankali mutum ya kirkiro na ilimi, hikima da dai sauransu, abubuwa ne da suke taimakawa, nesa ba kusa ba, wajen tabbatar da kyakkyawar rayuwa da kuma bube sabbin kofofin fahimtarta.
Don haka ne Alkur'ani mai girma yake shiryar da mu zuwa ga amfani da kwarewar al'ummomi da kuma daidaikun mutane bugu da kari kan tunani da kuma amfani da hankali. Allah Madaukakin Sarki Yana ce wa: "Kuma Shi ne Wanda Ya shimfida kasa, kuma Ya sanya duwatsu da koguna a
cikinta, kuma daga dukkan 'ya'yan itace Ya sanya ma'aura biyu cikinsu.
Yana sanya dare ya rufe yini. Lalle ne a cikin wancan, hakika akwai ayoyi ga mutane wakanda suke yin tunani". (Surar Ra'ad, 13: 3)
"Kuma ba Mu aika ba a gabanninka face mazaje, Muna wahayi zuwa gare su, daga mutanen kauyuka. Shin fa, ba su yi tafiya a cikin kasa ba, domin su duba yadda karshen wadanda suka kasance daga gabanninsu ta zama? Kuma lalle ne gidan Lahira shi ne mafi alheri ga wadanda suka yi takawa, shin fa, ba ku hankalta? Har a lokacin da Manzanni suka yanke tsammani, kuma suka yi zaton cewa an jingina su ga karya, sai taimakonMu ya je musu, sa’an nan Mu tserar da wanda Muke so, kuma ba a mayar da azabarMu daga mutane masu laifi. Lalle ne, hakika, abin kula ya kasance a cikin kissoshinsu ga masu hankali. Bai kasance wani kirkiran labari ba, kuma amma shi gaskatawa ne ga abin da yake a gaba gare shi, da rarrabewar dukkan abubuwa, da shiriya da rahama ga mutane wadanda suka yi imani”. (Surar Yusuf, 12: 109-111)
An ruwaito Imam Ali (a.s.) yayin da yake huduba ga dansa Imam Hasan (a.s.), yana shawartarsa da yin amfani da kwarewar sauran mutane, inda yake ce masa:
".....don ka shirya wa karbar kwarewar wasunka ta hanyar tunaninka, don ka tsira daga fadawa cikin abubuwan da suka fada. Ta haka sai ka tsere wa wahalar nemansa da kuma wahalar gwaji. Don haka, sai ka ga ka san abin da muka gani kana muka shaida da ma abubuwan da suka bayyana maka wadanda watakila mu ba mu riske su ba.....". [2]
Hakika a duk lokacin da muka samar wa kawukanmu ingantacciyar fahimta ta rayuwa, bisa ka'idojin shari'a, hankali da kuma ilimi, to za mu sami damar tafiyar da rayuwarmu cikin jin dadi da kuma nasara.


1. Al'Ya'akubi / juzu'i na 2 / hudubar ban-kwana /shafi na 110/ Dar Sadr - Beirut.
2. Nahjul Balagah / hadawar Dr. Subhi Salihi / shafi na 393.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
8+2 =