Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Kawo Mana Takaitaccen Bayani Game Da Tafsirin Kur’ani Mai Girma?


Hakika Mu ne muka saukar da (Littafin) Kur'ani kuma Mu masu kariya ne gareshi. Hijr: 9.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya saukar da littafi mabayyani domin ya kasance shiriya da haske ga halittun duniya, Kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga cikamakin Annabawa da manzanni, wanda aka aiko shi ya zama mai bushara da gargadi ga talikai, shugabanmu kuma Annabinmu Muhammad Al-mustafa da alayensa masu shiryarwa kuma tsarkaka
Bayan haka, hakika bukatuwar fassara kur’ani mai girma ba ta yankewa a kowane zamani, domin kuwa zamani yana sabuntuwa domin kodayaushe yana motsawa ne yana mai tafiya ba tare da tsayawa ba, kuma sababbun maudu’ai suna sake bubbugowa da kunno kai, ga kuma girma da kima da wannan littafin yake da shi, don haka rashin samun tafsiri daga ma’abota ilimi masu fahimtar wannan littafin kamar yadda ya zo daga Allah (S.W.T) da koyarwar Ahlul Baiti (A.S) to yana nufin hana biliyoyin ‘yan adam jin wannan haske da ya sauko daga ubangiji madaukaki, da hana su sanin manufar halittarsu da kuma nauyin da Allah (S.W.T) ya dora musu. Da kuma hana su sanin takamaiman hakikanin sakon da yake kunshe cikin wannan littafin kararre daga dukkanin kura-kurai kuma saukakke daga madaukaki mai baiwa, kuma mu’ujiza madawwamiya daga Allah domin kafa hujja kan bayinsa gaba daya, kuma rashin tafsirinsa kangiya ce daga sanin hadafin da yake dauke da shi na shiryarwa da haskakawa.

Tafsirin kur’ani yana iya nuna mana abubuwa kamar haka:
Nuni da fahimtar ayoyin Allah madaukaki: Ubangiji madaukaki yana fada a cikin littafinsa mai girma “Da sannu zamu nuna musu ayoyinmu a sasanni (sammai da kassai) da kuma a kawunansu, har sai ya bayyana gare su cewa shi (Ubangiji) gaskiya ne” Fusilat: 53.

Domin fassara da kur’ani mai girma akwai hanyoyi da malamai suka gabatar wadanda suka hada da:
Ta farko: Tafsirin Kur'ani da Kur'ani, wato fassara Kur'ani ta hanyar amfani da ayoyinsa;
Ta biyu: Yin tafsirin Kur’ani ta hanyar yin amfani da sunnar Annabi (S.A.W) tare da ruwayoyin da aka samo daga Imaman Ahlul Baiti (A.S.) Bisa dogaro da ruwayar nan mutawatira wacce littattafan hadisan dukkan bangarorin musulmi suke cike makil da ita, a inda Ma'aiki (S.A.W) yake cewa: Hakika ni na bar muku nauyaya guda biyu: Littafin Allah da zuriyata 'ya'yan gidana, domin lallai wadannan ababe biyu ba zasu taba rabuwa da juna ba har sai sun iske ni a tafkina (aljanna).
Wannan ruwayar ta zo cikin littafai da dama, ga kadan daga Irinsu:
1- Sahih Muslim babin falalar Ali bin Abi Talib
2- Musnad Ahmad bin Hanbal juzu'i na 4 shaft na 366
3- Sahih Tirmizi juzu'i na 13 shafi na 199 babin manakibu Ahlul Baiti (A.S)
4- Sunanul Baihaki juzu'i na 3 shafi na 148 da kuma juzu'i na 7 shafi na 30
5- Mustadrakus sahihain juzu'i na 3 shafi na 109
6- Usdul Gaba juzu'i na 2 shafi na 12
7- Hilyatul Auliya juzu'i na 1 shafi na 355
8- Tarikhu Bagdad juzu'i na 8 shafi na 442
9- Majma'uz zawa'id juzu'i na 9 shafi na 163
10-Kanzul Ummal juzu'i na 1 shafi na 48
11- As-sahawi fi mushkilil Asar juzu'i na 4 shafi na 368

Yana da kyau masu tafsirn Kur'ani da tarjama ma’anoninsa su yi amfani da yare mai sauki da zai iya isan da sakon ga dukkan samari da matasa domin ya kasance mai amfani ka kowane musulmi da yake neman sanin Kur'ani mai grima.
Wannan al’amari ya zama dole musamman da yake har yanzu a harshen hausa dukkan tafsirai da tarjamomin da aka yi ba su iya magance dukkan bukatun da al'ummar musulmi ke da su a yau ba, na daga abin da ya shafi ci gaban rayuwar zamani, saboda haka ne ma masu magana da wannan harshe ba su gushe ba suna bukatar sabon tafsiri na Kur’ani wanda zai bijiro da ilimin da zai warware muhimman abubuwan da musulmi suka isa gare shi na ci gaban rayuwa a harkoki daban daban, kamar yanda wannan, matsala ta bukatuwa ga samun sabon tafsiri na Hausa wanda ya dace da zamani ta fi shafan wadanda ba su jin yaren larabci kana ba su sanin tsofaffin kalmomin Hausa wadanda malamai magabata suka yi amfani da su a tafsirin Kur’ani da tarjamarsa .
An fara samun yunkuri da kokari daga al’ummarmu da muke fatan ya dore domin ganin an samu cigaba a tafsirin Kur'ani da tarjamarsa cikin harshe Hausa kamar yadda malamai marubuta littafin nan na “Rabi'ul Mu'uniinina fi tafsiril kitabil Mubin”. Wanda suka fassara cikin harshen na Hausa da ma’anar; “Dausayin muminai cikin tafsirin littafi mabayyani”. Kuma sun yi bayanin manhajar da suka bi cikin wannan tafsirin kamar haka: “Lallai mun bi hanyar fayyace ababen da suke bukatan bayani tare da bayyana mahangar Mazhabar Ahlul Bait (A.S.) na daga ababen da suka shafi: tarihi da akida, kana da tarbiyya da wanin wadannan, kamar yanda muka yi kokarin bayyana falalar surorin Kur’ani a farkon kowace sura bisa dogaro da hadisan da aka samo daga Annabi (S.A.W) da Ahlul Baiti (A.S.)”.

Surar Fatiha

1. Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai
2. Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai.
3. Mai rahama mai jin kai.
4. Mai mallakar ranar sakamako.
5. Kai kadai muke bautawa kuma kai kadai muke neman taimako.
6. Ka shiryar da mu tafarki madaidaici.
7. Tafarkin wadanda ka yi wa ni’ima, ba wadanda aka yi fushi. da su ba, kuma ba batattu ba.

Surar Nasi (Mutane)

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai
1. Ka ce ina neman tsari ga ubangijin mutane.
2. Mamallakin mutane.
3. Abin bautar mutane.
4. Daga sharrim mai waswasi mai boyewa.
5. Wanda yake sanya waswasi a cikin zukatan mutane.
6. Daga aljanu da mutane.
Surar Falaki (Asuba)
Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai
Ka ce ina neman tsari ga ubangijin safiya.
Daga sharrin abin da ya halitta.
Daga sharirn dare idan ya yi duhu.
Daga sharrin mata masu tofi a cikin kulle-kulle.
Daga sharrin mahassadi yayin da ya yi hassada.

Surar Tauhid (Kadaitaka)

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai
1. Ka ce Allah makadaici ne.
2. Allah ne manufar mabukata.
3. Bai haifa ba kuma ba a haife shi ba.
4. Kuma babu wani da ya kasance tamka a gareshi.

Surar Lahab (Harshen wuta)

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai
1. Hannaye biyu na AbuLahab sun halaka, kuma ya halaka.
2. Dukiyarsa da abin da ya tara ba sa tsare masa komai.
3. Zai shiga wuta mai huruwa.
4. Tare da matarsa mai daukar itacen wuta.
5. A cikin wuyanta akwai igiya takaba.

Surar Nasr (Cin nasara)

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai
1. Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara.
2. Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah jama’a-jama’a.
3. To, ka yi tasbihi da gode wa ubangijinka, kuma ka neme shi gafara, Lalle shi ya kasance mai yawan karbar tuba ne.

Surar Kafirun (Kafirai)

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai
1. Ka ce; ya ku kafirai.
2. Ba zan bauta wa abin da kuke bauta wa ba.
3. Kuma ba zaku zama masu bauta ga abin da nake bauta wa ba.
4. Kuma ni ba zan zama mai bauta wa abin da kuke bauta wa ba.
5. Kuma ku ba zaku zama masu bauta wa abin da nake bauta wa ba.
6. Addininku na gareku, kuma addinina na gareni.

Surar Kausar (Tafkin Kausara)

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai
1. Lalle ne mu, mun yi maka kyauta mai yawa.
2. Saboda haka ka yi salla domin ubangijinka, kuma ka yi suka (soke taguwa, rakumi).
3. Hakika mai aibata ka shi ne mai yankakken baya (maras albarka)

Surar Ma’un (Kayan taimako)

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai
1. Shin ka ga wanda yake karyatawa game da sakamako?
2. To wannan shi ne yake tunkude maraya.
3. Kuma ba ya kwadaitarwa bisa ciyar da miskini.
4. To azaba ta tabbata ga masallata.
5. Wadannan da suke masu shagala daga sallarsu.
6. Wadannan da sukeyin riya.
7. Kuma suna hana taimako.

Surar Kuraish (Kuraishawa)

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai
1. Saboda sabon kuraishawa.
2. Sabonsu na tafiyar hunturu da ta bazara.
3. Don haka sai su bauta wa ubangijin wannan dakin.
4. Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da su daga wani tsoro.

Surar Fil (Giwa)

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai
1. Ashe ba ka ga yadda ubangijinka ya aikata ga mutanen giwa ba?
2. Ashe bai sanya kaidinsu a cikin tabewa ba.
3. Kuma ya aika musu da wasu tsuntsaye gungu-gungu.
4. Suna jifarsu da wasu duwatsu na yumbun wuta.
5. Sai ya sanya su kamar karmami abin cinyewa.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
10+10 =